14. Yawo acikin Jeji

14. Yawo acikin Jeji — illustration 1

Bayanda Allah ya fada wa isra'ilawa dokokin da yake so su yi biyayya da su a matsayin alkawarin sa da su, suka tafi daga dutsen Sina'i. Allah ya fara jagorar su zuwa yankin kasar alkawari, wanda kuma ake kira kan'ana. Al'amudin girgije na tafiye a gabansu zuwa kan'ana su kuma suna biye da shi.

14. Yawo acikin Jeji — illustration 2

Allah yayi wa Ibrahim, Ishaku, da Yakubu alkawari cewa zai bada kasar alkawari ga zuri'ar su, amma yanzu akwai kungiyoyin mutane da yawa dake zaune a wurin. Ana kiran su kan'aniwa. Kan'aniwa basu bauta ko su yi biyayya da Allah ba. Suna bautar allolin karya kuma suna yin miyagun abubuwa da yawa.

14. Yawo acikin Jeji — illustration 3

Allah ya cewa Isra'ilawa, "Lalle ne ku kawar da dukkan Kan'aniwa acikin kasar alkawari. Kada ku yi yarjejjeniyar salama da su kuma kada ku aure su. Lelle ne ku hallakar da dukkan gumakunsu gabaki daya. Idan ba ku yi biyayya da ni ba, zaku bauta ma gumakunsu a maimako na."

14. Yawo acikin Jeji — illustration 4

Sa'anda Isra'ilawa suka iso gabar Kan'ana, Musa ya zabi mutum goma sha biyu, daya daga kowace kabilar Isra'ila. Ya basu umurni su je lekan asirin kasar su kuma gani yadda ta ke. Su kuma dubi yanayin Kan'aniwa su gani ko suna da karfi ko kasassu.

14. Yawo acikin Jeji — illustration 5

Mutanen nan goma sha biyu suka yi tafiya cikin Kan'ana kwana arba'in sa'an nan suka komo. Suka fada wa jama'ar, "Kasar na da albarka kuma ga yawan anfani!" Amma goma daga cikin masu lekan asirin suka ce, "Birnin na da karfin gaske kuma mutanen katti ne! Idan muka kai masu hari, tabbas zasu fi karfin mu kuma su kashe mu!"

14. Yawo acikin Jeji — illustration 6

Nan take Kalibu da Joshua, biyu daga cikin masu lekan asirin, suka ce, "Gaskiya ne mutanen Kan'ana dogi ne kuma karfafa, amma tabbas za mu sha karfin su, Allah zai yi yaki amadadin mu!"

14. Yawo acikin Jeji — illustration 7

Amma mutanen basu saurari Kalibu da Joshua ba. Suka yi fushi da Musa da Haruna suna cewa, "Me yasa kuka kawo mu wannan mummunar wuri? Da ma mun zauna a Masar maimakon a kashe mu cikin yaki kuma a maida matanmu da yayan mu bayi." Mutanen suna so su zabi wani shugaba dabam wanda zai komar da su Masar.

14. Yawo acikin Jeji — illustration 8

Allah ya husata kwarai har ma ya zo alfarwar saduwa. Allah yace, "Domin kunyi tawaye agare ni, dukkan mutane zasu yi famar yawo a daji. Banda Joshua da Kalibu, kowane daya dake shekara ashirin ko fiye zai mutu acan kuma ba zai taba shiga kasar alkawarin ba."

14. Yawo acikin Jeji — illustration 9

Da mutanen suka ji haka, suka tuba don sunyi zunubi. Suka dauki kayan yakinsu suka tafi domin su yaki mutanen Kan'ana. Musa kuwa ya gargade su kada su je domin Allah baya tare da su, amma basu saurare shi ba.

14. Yawo acikin Jeji — illustration 10

Allah bai tafi tare da su zuwa yakin ba, saboda haka aka yi nasara akan su kuma aka kashe da yawa acikin su. Sa'annan Isra'ilawa suka juya wa Kan'ana baya kuma su ka yi faman yawo a daji har shekaru arba'in.

14. Yawo acikin Jeji — illustration 11

Cikin shekaru arba'in da mutanen Isra'ila suka yi suna yawo a daji, Allah yana yi masu tanadi. Allah ya basu gurasa daga sama, da ake kira "Manna." Ya kuma aiko da yan tsalwa (wanda suke kananan tsuntsaye) a cikin taronsu domin su sami nama su ci. Cikin dukkan lokacin nan, Allah ya kare kayakinsu da takalmansu daga kodewa.

14. Yawo acikin Jeji — illustration 12

Allah kuwa cikin al'ajibinsa ya basu ruwa daga dutse. Amma duk da haka, mutanen Isra'ila suka yi gunaguni game da Allah da Musa. Duk da haka, adalcin Allah bisa alkawarinsa ga Ibrahim, da Ishaku da Yakubu bai sake ba.

14. Yawo acikin Jeji — illustration 13

Wani lokaci sa'adda mutanen suka rasa ruwa, Allah ya ce wa Musa, "Yi magana da dutse, ruwa kuwa zai fito daga ita." Amma Musa bai girmama Allah agaban dukkan mutanen ba ta wurin buga dutsen sau biyu da sanda amaimakon magana da ita. Ruwa kuwa ya fito daga dutsen domin kowa ya sha, amma Allah yana fushi da Musa kuma yace, "Bazaka shiga kasar alkawarin ba."

14. Yawo acikin Jeji — illustration 14

Bayan da Isra'ilawa suka yi ta zagaya acikin daji har shekaru arba'in, dukkan wadanda suka yi tawaye ga Allah sun mutu. Sa'annan Allah ya jagoranci mutanen zuwa iyakar kasar alkawari kuma. Musa kuwa ya tsufa sosai, sai Allah ya zabi Joshua ya taimake shi da shugabantar mutanen. Allah kuwa yayi wa Musa alkawari da cewa wata rana, zai aiko da wani annabi kamar Musa.

14. Yawo acikin Jeji — illustration 15

Sa'annan Allah ya ce wa Musa ya haura saman dutsen domin ya kalli kasar alkawarin. Musa kuwa ya kalla kasar alkawarin amma Allah bai yarda masa ya shiga ba. Sa'annan Musa ya mutu, Isra'ilawa kuwa suka yi makokinsa har kwana talatin. Joshua kuwa ya zama sabon shugabansu. Joshua shugaba ne nagari domin ya dogara kuma yana biyayya ga Allah.

Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Fitowa 16-17; Littafin Kidaya 10-14; 20; 27 Maimaitawar Shari'a 34

Read in the reader

Free to use, adapt, and share under an open license (CC BY-SA 4.0).