27. Labarin Basamare Nagari

27. Labarin Basamare Nagari — illustration 1

Wata rana, wani masanin shari'ar Yahudawa, ya zo wurin Yesu domin ya gwada shi, yana cewa, "Malam, me zan yi in gaji rai madawwami?" Yesu ya amsa, "Me aka rubuta a shari'ar Allah?"

27. Labarin Basamare Nagari — illustration 2

Gwanin a dokokin Allah ya ce, "Ku kaunaci Ubangiji Allahn ku da dukkan zuciyar ku, da ran ku, da karfin ku, da kuma hankalin ku. Ka kuma kaunaci, makwabcin ka kamar kanka." Yesu ya amsa, "Ka yi dai dai! Ka yi haka za ka rayu."

27. Labarin Basamare Nagari — illustration 3

Amma masanin shari'ar ya so ya tabbatar shi mai adali ne, sai ya sake yin tambaya, "Wanene makwabci na?"

27. Labarin Basamare Nagari — illustration 4

Yesu ya amsa wa masanin shari'ar ta wurin bada labari. "An yi wani Bayahude da yake tafiya akan hanya daga Urushalima zuwa Yariko."

27. Labarin Basamare Nagari — illustration 5

"Yayin da mutumin yake tafiya, 'yan fashi suka fada masa. Suka kwace duk abin da ye ke da shi, suka kuma yi masa duka har ya kusa mutuwa. Sa'anna suka yi tafiyar su."

27. Labarin Basamare Nagari — illustration 6

"Nan da nan bayan haka, wani Firist Bayahude tafiya ta kawo shi wannan hanyar. Da wannan shugaban adini ya ga mutumin da aka yi wa duka da fashi, sai ya bi gefe daya na hanyar, ya kyale mutumin nan dake bukatar taimako, ya ci gaba da tafiya.''

27. Labarin Basamare Nagari — illustration 7

"Jim kadan da yin haka, wani Balawe ya gangaro kan hanyar. (Lawiyawa sune kabilun Yahudawa wandanda ke taimakon firistoci a Haikali.) Balawen shima ya ketare gefen hanya, bai kula mutumin da haka yi wa fashi da duka ba."

27. Labarin Basamare Nagari — illustration 8

"Mutumin da ke biye akan hanyar kuwa Basamare ne. (Samariyawa sune zuriyar Yahudawa wadan da suka auri mutane daga wassu al'umma. Samariyawa da Yahudawa sun tsani juna.) Amma da Basamaren ya ga Bayahuden, ya yi juyayi domin sa. Sai ya lura da shi ya daure masa raunukansa."

27. Labarin Basamare Nagari — illustration 9

"Basamaren ya dauki mutumin nan ya sa akan jakin sa, ya kai shi wani masauki baki kusa da hanya inda ya kula da shi."

27. Labarin Basamare Nagari — illustration 10

Kashegari, Basamaren yana bukatar yaci gaba da tafiyar sa. Sai ya ba wa mai kula da masaukin kudi yace, 'Ka lura da shi, idan kudin da kashe yafi wannan, zan biya ka idan na dawo.'''

27. Labarin Basamare Nagari — illustration 11

Sa'annan Yesu ya tambayi masanin shari'ar, "Me kake tunani? A cikin mutanen nan uku, wanene makwabcin wanda aka yi wa fashi da duka?" Sai ya amsa. "Wanda ya yi masa jinkai." Yesu ya gaya masa, "Kaima jeka kayi haka."

Labari a Littafi mai Tsarki daga: Luka 10:25-37

Read in the reader

Free to use, adapt, and share under an open license (CC BY-SA 4.0).