8. Allah ya ceci Yusufu da Iyalinsa.

8. Allah ya ceci Yusufu da Iyalinsa. — illustration 1

Bayan shekaru da yawa, a lokacin Yakubu ya tsufa, ya aika kaunataccan dan sa Yusufu ya duba yan'uwansa wadan da ke kula da garkuna.

8. Allah ya ceci Yusufu da Iyalinsa. — illustration 2

'Yan'uwa Yusufu sun ki shi saboda mahaifinsu yafi kaunarsa kuma domin Yusufu yayi mafarki cewa, zai yi mulkinsu. Da Yusufu ya iso wurin 'yan'uwansa, suka kama shi kuma suka sayar da shi ga masu fataucin bayi.

8. Allah ya ceci Yusufu da Iyalinsa. — illustration 3

Kafin 'yan'uwan Yusufu su koma gida, suka yage tufafin Yusufu suka tsoma shi cikin jinin akuya. Suka nuna wa mahifinsu tufafin Yusufu tufafiinsa domin ya yi tunanin cewa dabban daji ne ya kashe Yusufu. Yakubu yayi matukar bakin ciki.

8. Allah ya ceci Yusufu da Iyalinsa. — illustration 4

Masu fataucin bayin kuwa suka kai Yusufu kasar Masar. Kasar masar kasa ce mai girma, da iko, kuma tana kusa da kogin Nilu. Masu fataucin bayin suka sayar da Yusufu bawa ga wani attajiri ma'aikacin gwamnati. Yusufu yayi wa mai gidansa bauta da kyau, Allah kuwa ya albarkace Yusufu.

8. Allah ya ceci Yusufu da Iyalinsa. — illustration 5

Matar mai gidansa ta nemi ta yi zina da Yusufu, amma Yusufu ya ki yayi wa Allah zunubi ta wanan hanya. Matan ta husata sa'annan ta yi wa Yusufu zargin karya aka kama shi aka kai shi kurkuku. Ko acikin kurkuku, Yusufu ya cigaba da amincinsa ga Allah, Allah kuwa ya albarkace shi.

8. Allah ya ceci Yusufu da Iyalinsa. — illustration 6

Bayan shakaru biyu, Yusufu na kurkuku, ko da shike shi ba mai laifi bane. A wata dare, Fir'auna, wanda shine yadda Masarawa ke kiran sarakunansu, ya yi mafarkai guda biyu da suka dame shi sosai. Ba wani a cikin mashawartansa da ya iya gaya masa ma'anar mafarkan.

8. Allah ya ceci Yusufu da Iyalinsa. — illustration 7

Allah kuwa yayi wa Yusufu baiwan fassaran mafarkai, saboda haka Fir'auna ya aika a kawo masa Yusufu daga kurkuku. Yusufu ya fassara masa mafarkan cawa, "A cikin shekaru bakwai, Allah zai aiku yalwatacce girbi, bayan haka za'a yi shakaru bakwai na yunwa."

8. Allah ya ceci Yusufu da Iyalinsa. — illustration 8

Yusufu ya burge Fir'auna har ya nada shi ya ya zama na biyu acikin wadanda suka fi iko a dukkan Masar.

8. Allah ya ceci Yusufu da Iyalinsa. — illustration 9

Yusufu ya ce wa mutanen su yi ajiyan abinci da yawa a lokacin shakarun nan bakwai na kyakkyawan girbi. Sai Yusufu yana sayar da abinci ga mutane sa'anda shakaru bakwai na yunwa ya zo domin su sami isasshen abinci su ci.

8. Allah ya ceci Yusufu da Iyalinsa. — illustration 10

Yunwan ta yi tsanani ba'a Masar kadai ba, amma har Kan'ana inda Yakubu da Iyalinsa suke zama.

8. Allah ya ceci Yusufu da Iyalinsa. — illustration 11

Sai Yakubu ya aiki mayan 'ya'yansa maza zuwa Masar su sayo abinci. Yan'uwan ba su gane Yusufu ba yayin da suka tsaye a gabansa domin tsayen abinci. Amma Yusufu ya gane su.

8. Allah ya ceci Yusufu da Iyalinsa. — illustration 12

Bayan ya gwada yan'uwansa ya gan ko sun canza, Yusufu ya ce masu, "Ni ne dan'uwan ku, Yusufu! Kada ku ji tsoro. Kun yi niyar yin mugunta sa'anda kuka sayar da ni bawa, amma Allah ya yi anfani da muguntar ya zama alheri! Ku zo ku zauna a Masar domin in tanada maku da Iyalanku."

8. Allah ya ceci Yusufu da Iyalinsa. — illustration 13

Sa'anda yan'uwa Yusufu suka komo gida, suka fada wa mahifinsu, Yakubu, cewa Yusufu na da rai, ya yi faran ciki sosai.

8. Allah ya ceci Yusufu da Iyalinsa. — illustration 14

Ko da shike Yakubu ya tsufa, ya tafi Masar da dukkan iyalansa, suka kuma zauna acan. Kafin mutuwan Yakubu, ya albarkaci kowane dansa.

8. Allah ya ceci Yusufu da Iyalinsa. — illustration 15

Wa'adin alkawaran da Allah ya yi wa Ibrahim an mika wa Ishaku sa'annan ga Yakubu, da kuma 'ya'yan Yakubu goma sha biyu da iyalansu. Zuri'ar 'ya'ya goma sha biyun suka zama kabilu goma sha biyu na Isra'ila.

Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Farawa 37-50

Read in the reader

Free to use, adapt, and share under an open license (CC BY-SA 4.0).