32. Yesu ya Warkar da Mutum mai Aljannu da Mace Marar Lafiya

32. Yesu ya Warkar da Mutum mai Aljannu da Mace Marar Lafiya — illustration 1

Wata rana, Yesu da almajiransa suka ketare tafki a cikin jirgin ruwa zuwa wa lardin da mutanen Garisinawa ke zama.

32. Yesu ya Warkar da Mutum mai Aljannu da Mace Marar Lafiya — illustration 2

Da suka kai daya bangaren tafkin, sai wani mutum da aljannu suka mallake shi ya rugo a guje zuwa wurin Yesu.

32. Yesu ya Warkar da Mutum mai Aljannu da Mace Marar Lafiya — illustration 3

Wannan mutum yana da karfi sosai, har ma babu mai ikon bi da shi. Har ma mutane sun sa masa sarka a hannaye da kafafu, amma ya yi ta tsintsinke su.

32. Yesu ya Warkar da Mutum mai Aljannu da Mace Marar Lafiya — illustration 4

A makabarta mutumin yake zama. Mutumin yakan yi kururuwa dukan dare da dukan rana. Ba ya sa tufafi yana ta yanka jikinsa da duwatsu kullum.

32. Yesu ya Warkar da Mutum mai Aljannu da Mace Marar Lafiya — illustration 5

Da mutumin ya zo wurin Yesu, sai ya fadi a gwiwarsa a gaban sa. Yesu ya ce wa aljannin, "Fita daga cikin wannan mutumin!"

32. Yesu ya Warkar da Mutum mai Aljannu da Mace Marar Lafiya — illustration 6

Mutumin nan mai aljanni yayi kuka da murya mai karfi, "Me kake so da ni, Yesu, Dan Allah Madaukaki? Ina rokonka kada kayi mani azaba." Sai Yesu ya tambayi aljannin, "Menene sunan ka?" Ya amsa, "Suna na Tuli, domin muna da yawa." ("Tuli" jimla ce ta rundunar sojoji dubun dubbai na mayakan Romawa.)

32. Yesu ya Warkar da Mutum mai Aljannu da Mace Marar Lafiya — illustration 7

Aljannun suka roki Yesu, "Muna rokonka kada ka kore mu daga wannan lardin!'' Akwai wani garken aladu da ke kiwo a wani tudu kusa da wurin. Sai, aljannun suka roki Yesu, "A maimakon haka ka tura mu cikin aladun nan in ka yarda!" Yesu ya ce, "Tafi!"

32. Yesu ya Warkar da Mutum mai Aljannu da Mace Marar Lafiya — illustration 8

Aljannun sun fita daga mutumin sun shiga cikin aladu. Aladun kuwa suka ruga sai cikin tafki, a inda suka hallaka. Garken aladun kuwa sun kai 2,000.

32. Yesu ya Warkar da Mutum mai Aljannu da Mace Marar Lafiya — illustration 9

Da makiyan aladun suka ga abin da ya faru, sai suka ruga cikin gari, suka gaya wa duk wanda suka gani abin da Yesu ya yi. Mutanen garin suka fito, suka ga mutumin da ke da aljannu a da. Yana zaune a natse, yana cikin hankalinsa, yana kuma sanye da tufafi.

32. Yesu ya Warkar da Mutum mai Aljannu da Mace Marar Lafiya — illustration 10

Mutanen sun ji tsoro kwarai, sun roki Yesu ya rabu da su. Sai Yesu ya shiga jirgin ruwa da shirin tafiya. Mutumin da ke da aljannun a da, ya roka ya tafiya tare da Yesu.

32. Yesu ya Warkar da Mutum mai Aljannu da Mace Marar Lafiya — illustration 11

Amma Yesu ya ce masa, "A'a, Ina so ka je gida ka fada wa abokan ka da iyalin ka dukan abin da Allah yayi maka, da kuma yadda ya nuna maka jinkai."

32. Yesu ya Warkar da Mutum mai Aljannu da Mace Marar Lafiya — illustration 12

Mutumin ya tafi, ya kuma fada wa kowa da kowa abin da Yesu yayi masa. Duk wanda ya ji labarinsa, ya cika da mamaki da al'ajibi.

32. Yesu ya Warkar da Mutum mai Aljannu da Mace Marar Lafiya — illustration 13

Yesu ya koma wancan bangare na tafkin. Da isowarsa can, taron jama'a masu yawa suka taru kewaye da shi, suka matse shi. A taron jama'ar kuwa, akwai wata mace wanda ta wahala sosai da damuwa na zubar da jini har na shekaru goma-sha-biyu. Ta kashe kudin ta duka wurin likitoci don su warkar da ita, amma damuwar sai kara muni yayi.

32. Yesu ya Warkar da Mutum mai Aljannu da Mace Marar Lafiya — illustration 14

Ta ji cewa Yesu ya warkar da marasa lafiya da yawa, a cikin tunaninta ta ce, "Na tabbata idan har na iya taba tufafin Yesu kawai, ni ma zan warke!" Sai ta zo ta bayan Yesu, ta taba tufafin sa. Da zaran ta taba su, sai zuban jinin ya tsaya!

32. Yesu ya Warkar da Mutum mai Aljannu da Mace Marar Lafiya — illustration 15

Nan da nan, Yesu ya gane da cewa iko ya fita daga gareshi. Sai ya juya yayi tambaya, "Wa ya taba ni?" Almajiran suka amsa, "Mutane da yawa ke anan, gasu nan kewaye da kai har turin ka suke yi. Me ya sa ka yi tambaya, 'Wa ya taba ni?'"

32. Yesu ya Warkar da Mutum mai Aljannu da Mace Marar Lafiya — illustration 16

Macen nan ta fadi a kan gwiwowinta a gaban Yesu, tare da tsoro da rawan jiki. Sai ta fada masa abin da ta yi, da kuma cewa ta sami warkaswa. Yesu ya ce ma ta, "Bangaskiyar ki ya warkar da ke. Ki tafi cikin salama."

Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Matta 8:28-34; 9:20-22; Markus 5:1-20; 5:24b-34; Luka 8:26-39; 8:42b-48

Read in the reader

Free to use, adapt, and share under an open license (CC BY-SA 4.0).