33. Labarin Manomi

33. Labarin  Manomi — illustration 1

Wata rana, Yesu na koyar da taro mai yawan gaske kusa da bakin tafki. Sai mutane da yawa suka zo su saurare shi, har Yesu ya shiga jirgin ruwa a iyakan ruwan domin dai ya sami sarari yayi magana da su. Ya zauna cikin jirgin ya koyar da mutanen.

33. Labarin  Manomi — illustration 2

Yesu ya fadi wannan labari. "Wani manomi ya tafi ya shuka wassu iri. Da yake watsar da irin da hannu, wassu irin suka fada a kan hanya, tsuntsaye kuma sun zo suka tsince irin duka."

33. Labarin  Manomi — illustration 3

"Wassu irin kuma sun fada a cikin duwatsu, inda babu kasa sosai. Irin da ke cikin duwatsun suka tashi da sauri, amma saiwarsu basu iya shiga da zurfi cikin kasa ba. Da rana ya taso yayi zafi, shukin suka yankwane suka mutu."

33. Labarin  Manomi — illustration 4

"Har yanzu wassu irin suka fada tsakanin kayayuwa. Irin nan suka fara yin girma, amma kayayuwa suka shake su. Saboda haka shukin da suka yi girma daga irin nan da aka shuka cikin kayayuwa basu ba da wani kwaya ba."

33. Labarin  Manomi — illustration 5

"Wassu iri kuwa suka fada a cikin kasa mai kyau. Irin nan suka yi girma, suka kuma ba da amfani ribi 30, 60, har ma 100 kamar yawan iri da aka shuka. Mai kunnen ji, ya ji!"

33. Labarin  Manomi — illustration 6

Wannan labarin ya rikitar da almajiran. Saboda haka Yesu ya bayyana, "Irin nan kalmar Allah ne. Hanyan nan kuma mutum ne wanda ya ji kalmar Allah, amma bai gane ba, sai shaidan ya dauke kalmar daga gareshi."

33. Labarin  Manomi — illustration 7

"Kasa mai duwatsun nan kuma, mutum ne wanda ya ji kalmar Allah, ya kuma karbe shi da murna. Amma da ya da ji wahala ko tsanani, sai ya fadi."

33. Labarin  Manomi — illustration 8

"Kasa mai kayayuwa, mutum ne wanda ya ji kalmar Allah, amma da lokaci na wucewa, kwadayin kayan duniya, arziki, da kuma anashuwa na wannan rayuwa suka shake kaunar Allah a cikin sa. Sakamakon haka, koyarwa da ya ji bai ba da 'ya'ya ba."

33. Labarin  Manomi — illustration 9

"Amma kasa mai kyau, mutum ne wanda ya ji kalmar Allah, ya gaskanta shi, ya kuma ba da 'ya'ya."

Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Matta 13:1-8, 18-23; Markus 4:1-8, 13-20; Luka 8:4-15

Read in the reader

Free to use, adapt, and share under an open license (CC BY-SA 4.0).